fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ba mutanen da harin jirgin ƙasa ya shafa kyautar miliyan 50

Ƙaungiyar Gwamnonin Najeriya ta NGF ta bai wa waɗanda harin jirgin ƙasa a Kaduna ya ritsa da su kyautar naira miliyan 50.

Wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na ƙungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar ranar Juma’a ta ce shugaban NGF, Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi ne ya miƙa kyautar kuɗin ga gwamnatin Jihar Kaduna.

Gwamnan ya ba da kuɗin ne a ziyarar da ya kai wa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ranar Juma’a.

Fayemi ya ce sun kai ziyarar ce don su jajanta wa gwamnati da kuma mutanen da harin ya shafa, wanda ya kashe mutum aƙalla takwas da sace wasu kusan 100.

Karanta wannan  TO FA: Dan takara ya kwace motocin da ya rabawa deligate bayan ya fadi zaben fidda gwani a PDP

Ya siffanta harin da “mai kaɗa zuciya” saboda yawan waɗanda lamarin ya ritsa da su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.