fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Ƴan bindiga sun kashe mutane ukun da suka yi garkuwa da su bayan sun karɓi kudin fansa a Kaduna

Wasu ƴan bindiga da suka sace wasu mazauna Anguwan Bulus da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun kashe mutum uku cikin wadanda suka sace.

Sun kuma yi barazanar kashe sauran mutanen da ke hannunsu idan ba a biya su kudin fansa ba.

Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Kaduna ASP Mohammed Jalinge ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana cewa “An kira ni ta wayar tarho cewa an gano gawarwakin wasu mutum uku a cikin daji kusa da kauyen Dutse. AAn kai gawarwakin zuwa asibitin Saint Gerald Hospital.”

Karanta wannan  Zamu kubutar da fasinjojin jirgin kasa da aka sace amma muna bi a hankaline>>Fadar Shugaban kasa

Jaridar Vanguard ta Najeriya ta ce kimanin mako biyu da ya gabata ne wasu barayin daji suka kai hari a Anguwan Bulus kuma suka kashe wani mazaunin unguwar bayan sun sace wasu mutane masu dama.

Jaridar ta kuma ce maharan sun kuma kai hari a unguwannin Juji da Anguwan Gimbiya da Sabo GRA.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.