Thursday, July 18
Shadow

Ƴan bindiga sun kashe sojoji shida a wani hari kan bututun mai a Nijar

Wasu ƴan bindiga sun kai wa wata tawagar sojoji da ke sintirin aikin sa ido kan bututun man fetur a garin Tibiri da ke yankin Dosso a kudu maso yammacin Nijar harin kwantan ɓauna inda suka kashe sojoji akalla shida.

Rahoton wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta ya kara da cewa soja ɗaya ya ɓata sannan an lalata motoci biyu a harin.

Rahoton bai bayyana ko an samu asarar rai a ɓangaren ƴan bindigar ba, ko kuma bayyana alakarsu da wasu ƙungiyoyi.

Ƴan bindiga dai sun kasance suna gudanar da ayyukansu a wasu sassan Nijar da ke kan iyaka da arewa maso yammacin Najeriya.

Har yanzu dai rundunar sojin ƙasar ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba.

Karanta Wannan  Tsananin Rashin Tausayi: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, al’amuran tsaron ƙasar Nijar ke ƙara taɓarɓarewa, inda a lokuta da dama kungiyoyin masu dauke da makamai da masu iƙirarin jihadi ke kai hari kan jami’an tsaro da fararen hula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *