Ƴan Bindiga Dauke Da Bindigogi Sun Kutsa Gidan Malam Muttaka Safana Dake Karamar Hukumar Safana Ta Jihar Katsina Suka Sace Shi Da Amaryarsa Da Sati Ukku Da Yin Aurensu A Ranar Alhamis Da Ta Gabata.
Majiyar RARIYA Ta Nakalto Cewa Yan Bindigar Da Suka Sace Su, Sun Bugo Waya, Inda Suka Nemi A Biya Kuɗin Fansa Har Naira Miliyan 20 Kana Su Sako Su.
Allah Ya Bayyanar Da Su Cikin Aminci!
Daga Jamilu Dabawa, Katsina