Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace mutum biyar a hare-hare daban-daban da suka kai a ƙananan hukumomi biyu na Jihar Kwara.
Gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito cewa harin na farko ya faru ne a Egbejila da ke kan hanyar ƙauyen Obate duk a Ƙaramar Hukumar Asa.
A yayin harin, an sace wani tsohon mataimakin kwanturola na kwastam mai suna Mohammed Zarma wanda aka sace shi a gonarsa yake kiwon kifi.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kutsa gonar ne da bindigogi ƙirar AK-47 inda suka yi awon gaba da shi cikin daji.
Ɗayan harin ya faru ne a kan hanyar Obo Aiyegunle zuwa Osi da ke Jihar Ekiti inda ƴan bindigan suka sace wani bakanike da matarsa mai juna biyu da wasu mutum biyu da ke koyon sana’ar kanikanci.