fbpx
Saturday, March 25
Shadow

Ƴan Bindiga Sun Sace Uwa Da Yaranta Uku A Jihar Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

A daren jiya ne yan bindiga dauke da bindigogi suka kai a cikin garin Funtua a jihar Katsina inda suka sace matar aure Badiyya Shamsu Muhammad Kalgo da Ƴayanta ukku dake zaune a rukunin gidajen Jikan Malam dake Jabiri a karamar hukumar Funtua.

Majiyar RARIYA ta shaida mata cewa yan bindiga sun samu nasarar kutsawa gidan Malam Shamsudeen Muhammad Kalgo da Misalin karfe dayan daren jiya Litinin, inda suka tafi da Matarsa Malama Badiyya Shamsu da danta Almustapha Shamsu dan Shekara 12 zuwa 13 da diyarta Zainab yar Shekara tara da diyarta Halima Siyama Shamsu yar Shekara Shidda.

Karanta wannan  HOTUNA: Sanata Kwankwanso ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan Maragayi Sani Abacha, bisa rasuwar ɗansu Abdullahi Sani Abacha, wanda ya rasu a makwannin baya. Maryam Abacha matar Maragayi Sani Abacha ce ta tarbe su a gidansu da ke Abuja

Majiyar ta kara da cewa har zuwa haɗa wannan rahoto waɗannan bayin Allah na hannun yan bindiga kuma tun jiya da suka kira Malam Shamsu da daren ba su kara tuntubar su ba.

Allah Ya Bayyanar Da Su Cikin Aminci!

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *