
Haɗakar ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta Abuja ta dakatar da ayyukanta domin tantance ma’aikatanta.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Salisu Umar ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne domin tsaftace kasuwar.
Ya ce dama sukan yi haka lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ingancin sana’ar tasu.
Wakiliyar BBC da ta ziyarci kasuwar da ke unguwar Zone 4 a tsakiyar birnin Abuja, ta ce duka shaguna manya da ƙanana a kasuwar sun kasance a rufe.