fbpx
Saturday, June 25
Shadow

‘Ƴan Najeriya sun kashe sama da naira biliyan 100 kan ilimi a ƙasashen waje cikin wata uku’

Wata ƙididdiga daga Babban Bankin Najeriya wato CBN ta nuna cewa ƴan Najeriya sun kashe aƙalla dala miliyan 220.86 kan karatu a ƙasar waje daga Disambar 2021 zuwa Fabrairun 2022.

Hakan na nufin sun kashe sama da naira biliyan 100 a kuɗin Najeriya.

Jaridar Punch a ƙasar ta ruwaito cewa CBN bai bayyana adadin da yan ƙasar suka kashe a watan Maris da Afrilu da Mayu ba, inda bankin ya ce akwai yiwuwar adadin da ya fitar na daga Disambar 2021 zuwa Janairun 2022 a samu sauyi.

Karanta wannan  Burina Idan Kwankwaso Ya Zama Shugaban Kasa A 2023 Ya Soke Lefe Domin Matasa Su Samu Damar Yin Aure Cikin Sauki, Don Na San Shine Shugaban Da Zai Iya Duba Wannan Lamari, Cewar Tukur Nasiru

Ɓangaren ilimi musamman na jami’o’i a Najeriya na cikin wani hali sakamakon irin yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.