Tuesday, January 14
Shadow

Ƴan sintiri sun ceto mutum 63 a hannun masu garkuwa a Sokoto

Tawagar ƴan sintiri a jihar Sokoto ta ce ta kuɓutar da mutum 63 daga hannun masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, a jihar mai fama da matsalar ayyukan ƴan bindiga.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun Garba Mohammed, mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar ta ce tawagar ta ƙunshi jami’an ƴansanda da jami’an tsaro ƙarƙashin gwamnatin jihar Sokoto.

Bayanin ya bayyana cewa an kuɓutar da mutanen ne a tsawon kwana huɗu, daga ranar Lahadin da ta gabata.

Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan jirgi marar matuki da B0K0 Hàràm suka kaiwa sojoji hari dashi a jihar Borno

Haka nan a baya-bayan nan an samu ɓullar wata ƙungiyar ƴan bindiga da ake kira Lakurawa.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta tsananta ayyukan yaƙar ƴan bindiga tun bayan ɓullar ƙungiyar ta Lakurawa a ƙarshen shekarar da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *