fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Ƴan vigilante sun kama matasa su na feɗe doki domin siyar da naman ga al’umma a Kano

Ƴan vigilante sun kama matasa su na feɗe doki domin siyar da naman ga al’umma a Kan

Rundunar Vigilante, reshen unguwar Kundila sun cafke wasu samari da su ka yanka wani doki a Jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an kama samarin ne su uku yayin da su ke feɗe dokin a cikin wani aji a Makarantar Ƴar Kasuwa Firamare da ke Kundila, Ƙaramar Hukumar Tarauni a jiya Litinin.

Ibrahim Muhammad, Mataimakin Shugaban Vigilante na Kundila, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar sa wasu ƴan unguwar ne da su ka ga yaran shine su ka kawowa ofishin nasu rahoto, inda ya ƙara da cewa jami’an su ba su yi wata-wata ba su ka garzaya wajen.

Da isar jami’an wajen, a cewar Muhammad, sai kuwa su ka iske yaran na feɗe dokin, inda kan ka ce kwabo sun cafke su dukka ukun.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya zata rika biyan tsohon shugaban kungiyar MEND dake satar danyen man Fetur Biliyan 4 duk wata dan ya hana satar danyen man

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa samarin sun feɗe dokin ne domin sayar da naman ga al’umma a jihar.

Muhammad ya ce tuni dai su ka tattara bayanan farko kuma za su miƙa samarin ga ƴan sanda domin faɗaɗa bincike, inda a hakan za a gano ko ma sato dokin su ka yi ko akasin haka.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Mazhabobin addinin Musulunci sun bambanta wajen halaccin cin doki.

Amma a Mazhabar Imam Malik, wacce yawanci ita al’ummar Musulmin Nijeriya da ma Afirka su ke bi, cin naman doki Makhruhi ne, ma’ana abu ne maras kyau a addini.

Sai dai kuma wasu Mazhabobin sun riƙe ra’ayin cewa cin doki halal ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.