fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Ɓantanci wa manzon Allah (SAW) Gwamna Bala ya Gargadi Al’umma

Ɓantanci wa manzon Allah (SAW) Gwamna Bala ya Gargadi Al’umm

Daga Kamal Aliyu Bauchi.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da inganta tsaron lafiya da dukiyar al’umar jiha kana yace duk wani zance ko aikin da ya shafi ɓatanci ga Annabin rahama, Muhammadu ɗan gatan Allah abin Allah-wadai ne.

Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin ziyarar gaggawa a ƙaramar hukumar Warji inda aka samu tashin-tashina bisa zargin aibanta Manzon Allah (SAW).

A cewar Gwamna Muhammad, gwamnatin sa ko kusa ba za ta lamunci tozarta wani addini ko ta-da-zaune-tsaye ba kana gargaɗi al’umar jihar Bauchi da su zauna lafiya tare da mutunta juna inda ya ƙara da cewa za’a tabbatar da hukunta waɗanda ke zagon-ƙasa ga kwanciyar hankula da walwalar al’umar jiha.

Gwamnan sai yayi kira ga mutanen Warji da su martaba ƙaramar hukumar su da tayi fice wajen zaman lafiya tare da kira ga shugabannin addinai da su tabbatar da haɗin kai tare da watsi da kalaman muzanta juna.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: INEC ta bayyana sunayen 'yan takarar sanatoci amma ta cire Ahmad Lawal da Godswill Akpabio

A cewar gwamnan tuni gwamnatin sa da haɗin guiwar jami’an tsaro ta kafa kwamitin zaƙulo, gurfanar tare da hukunta waɗanda aka samu da laifin don kaucewa afkuwar irin sa a gaba.

Yace inganta walwala da zamatakewa na cikin ababen da gwamnatin sa ta sanya a gaba, a saboda haka za ta tabbatar da an daina zaman ɗar-ɗar a yankin biyo bayan waƙi’ar.

Shima da yake tofa albarkacin bakin sa, kwamishinan ƴan sanda na jihar Bauchi Umar Sanda cewa yayi rundunar ta himmatu wajen bada tsaro ga al’umar Bauchi da Najeriya.

A nasa ɓangaren kuwa, Hakimin Warji Alhassan Samaila, yabawa gwamnan yayi kan ziyarar.

Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani
21 Mayu, 2022.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.