fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ɓarayi Sun Harbi Mutum Daya Tare Da Ƙwace Ƙudaɗen Hannunsa A Jihar Katsina

Ɓarayi Sun Harbi Mutum Daya Tare Da Ƙwace Ƙudaɗen Hannunsa A Jihar Katsina

Daga Comr Nura Siniya

Wasu ɓarayi da ake zaton ƴan fashi da makami ne sun buɗewa wani ma’aikaci a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina wuta mai suna Aminu Darma, inda suka harbe shi a hannu bayan ya fito daga banki ɗauke da kuɗaɗe a cikin motarsa.

A rahoton da muka samu Barayin sun ci galaba akan Aminu Darma, ne a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa bayan ya fahimci suna biye dashi wanda har ya kai shataletalen (KSRC) dake kan hanyar zuwa Kano, yai sauri ya juya ya koma cikin gari, inda suka sake biyo shi wanda hakan yasa motar ta ƙwace mashi ta bugi wani ƙarfe ta tsaya.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

“Anan ne motar ta tsaya suka harbe shi a hannu tare da ƙwashe kuɗaɗen da yake ɗauke dasu a cikin a motar suka arce dasu. wanda yanzu haka yana ƙwance yana samun sauƙi a asibitin koyarwa na Jami’ar Ummaru Musa Yar’adua, dake cikin garin Katsina, kamar yadda wani makusancin shi Mai Wada ƊanMallam ya bayyana.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12pm. na rana, a daidai garejin Mashasha dake cikin birnin katsina.

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.