Aminu ya koma makaranta
Ɗalibin nan Aminu Adamu ya koma makarantarsu ta jami’ar tarayya da ke Dutse domin ci gaba da karatu bisa rakiyar ƴan ƙungiyar dalibai.

Da yammacin Asabar Aminun ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, inda ya samu tarba daga ƙungoyin ɗalibai na makarantu daban-daban.
Freedom Radio ta bi tawagar da ta raka ɗalibin daga Kano zuwa jami’ar tarayyan ta Dutse.
Ƙarin bayani zai zo nan gaba, har ma da jawaban da aka gabatar yayin tarbarsa.
Daga Freedom Radio