fbpx
Friday, February 26
Shadow

Ɗan Najeriya Kamaru Usman ya kafa tarihi a damben ajin welterweight bayan doke abokin karawarsa, Gilbert Burns

Ɗan Najeriya Kamaru Usman ya kare kambunsa na UFC, wato wasan da ake dambe da harbi da kafa ajin welterweight nauyin kilo sama da 77 bayan ya doke Gilbert Burns a faɗan da suka yi ranar Lahadi.

Da farko Usman, mai shekara 33 ya ji jiki hannun abokin dambensa ɗan Brazil wanda tsohon abokin atisayensa ne.

Amma daga baya ɗan damben na Najeriya ya farfaɗo ya doke abokin karawarsa mai shekara 34 tare da kare kambunsa na UFC a Las Vegas.

Ya lashe dukkanin damben da ya yi 13 na ajin UFC inda ya kere Georges St-Pierre wanda ya fi yawan nasara a welterweight.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *