fbpx
Saturday, May 21
Shadow

“Na san cewa kunada yaronku dake neman takarar shugabancin Najeriya, amm ni nafi cancanta”>>Amaechi ya fadawa wakilan APC na jihar Ogun

Tsohon gwamnan jihar Rivera kuna ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa yanada kwarewar da zai iya sgugabancin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a daren ranar litinin yayin dayake ganawa da gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun tare da wakilan APC na jihar.

Amaechi ya bayyana masu cewa ya san ‘yan jihar nada yaronsu dake muman takarar shugabancin Najeriya, watau mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo.

Amma duk da haka ya fada masu cewa shine yafi dacewa da shugabacin Najeriya domin kasar na bukatar shugaba irin shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.