fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Sojojin haɗin gwiwa sun ce sun fatattaki sansani 10 na ‘yan Boko Haram

Rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) mai yaƙi da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ta ce ta tarwatsa sansanin ƙungiyar 10 a arewa maso gabashin Najeriya.

Dakarun rundunar da suka ƙunshi sojojin Nijar da na Najeriya, da kuma dakarun rundunar Operation Hadin Kai ta Najeriya, sun fara aikin ne ranar Talata da ta wuce.

Wata sanarwa daga kakakin MNJTF, Kanar Kamarudeen Adegoke, ta ce dakarunsu sun gudanar da aikin fatattakar ‘yan Boko Haram a garuruwan Grada, da Kwatan Maishayi, da Daban Karfe, da Daban Gajere, da Tumbun Buhari da kuma Tunbun Abuja.

Karanta wannan  Nasan ku jajirtattu ne ku riga kora 'yan bindiga idan sun kawo maku farmaki, Gwamnan jihar Ondo ya fadaw 'yan jiharsa

Sai dai sanarwar ta ce dakaru ba su fafata da “ƴan ta’addan” ba saboda sun gudu daga sansanonin nasu a lokacin sharar.

Ya ƙara da cewa sojoji sun yi nasarar ɗebe makamai daga wuraren, ciki har da katan-katan na kifi, da hatsi, da kuma babur.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.