Kungiyar dake kare hakkin bil’adama ta SERAP ta bukaci shugaban hukumar zabe farfesa Mahmud Yakubu ya hukunta masu sayen kuru’u a zaben gwamnan jihar Ekiti da akayi.
Kwanaki bakwai kacal kungiyar ta bashi kuma tace idan hukumar zaben bata hukunta masu sayen kuru’un ba to su zasu fuskanci hukunci mai tsanani.
Kuma kungiyar ta bukaci hukumar zaben data gabatar da mutanen data kama a filin zaben a gaban kulliya domin a hukuntasu tare da masu daukar nauyin su.