Haramtacciyar kungiyar Biafra wacce akafi sani da IPOB ta musance cewa ita ce ke kashe mutane babu dalili a kudancin Najeriya.
Ta bayyana hakan ne bayan kungiyar ‘yan ta’addan Jamar Ansarul Muslimina fi Biladi Sudan wacce akafi sani da Ansaru ta bayyana cewa sunw kw kashw mutane a kudancin kasar nan.
Inda IPOB din ta bayyana cewa ita ba zata yu musu da Ansaru ba saboda ‘yan ta’adda ne amma kar su damu masu daukar nauyinsu sun kusa sauka daga mulki.
Kuma kungiyar ta musanta kashe mata me ciki da yaranta hudu a jihar Anambra, tace Fulanj zasu dandana kudarsu domin basu kadai ne keda Najeriya ba.