fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Da Dumi Duminsa: Mai martaba sarkin Katsina yace ba zai yi Hawan Daushe da babbar Sallah ba

Mai martaba sarkin jihar Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya bayyana cewa ba za ayi Hawan Daushe ba a babbar Sallah mai zuwa.

A yau ranar talata ne mai martaba sarkin ya isar da wannan sakon ne wanda ya fito ta hannun mataimakin sakataren fada, Mamman Dee.

Mamman Dee yace mai martaba sarkin Katsina yace Sallar Idi kawai zaiyi a ranar asabar amma banda Hawan Daushe.

Kuma yace dalili shine matalar tsaron da ake fama dashi a jihar, kuma yana kira ga al’umma suyi addu’a Allah ya kawo mana saukin matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.