‘Yan bindiga sun kashe kansilan gundumar Gudu Mboi kuma mataimakin shugaban karamar hukumar Song a jihar Adamawa.
‘Yan bindigar sun kashe shine a safiyar yau bayan sun dauke shi daga gidansa inda suka harne shi ya mutu bayan sjn tafi dashi.
Kuma ‘yan bindigar sun harbi yaronsa wanda yanzu hake yake asibiri likitoci na duba lafiyarsa.
Hukumar ‘yan sandan jihar ta tabbatar dafaruwar wannan lamarin kuma tace hukumar ta umurci a gaggauta nemo mutanen da suka aikata laifin don a hukunta su.