Kungiyar dake kare hakkin bil’adama ta SERAP ta maka hukumar zabe ta INEC a kotu kan taki kama ‘yan siyasar da suka sayi kuru’u a zaben jihar Ekiti.
Rahotannni da dama sun bayyaana cewa ‘yan takara sun sayi kuru’u sosai a zaben da aka gudanar na jihar Ekiti a makonnin da suka gabata.
Inda har aka samu labari cewa akwai wata jam’iyyar dake sayen kuru’u naira 10,000. A karshen zaben dai dan takarar APC Abiodun Oyebanji ne yayi nasarar lashe zaben da kuru’u 187, 057.
Kuma yanzu a ranar juma’ar data gabata SERAP ta maka hukumar zabe ta INEC a kotu kan taki kama ‘yan takarar da suka sayi kuru’u a zaben.