Mai martaba sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk ya angwance da sabuwar amaryarsa Aisha Yahuza Gona.
An daure auren ne a karamar hukumar Safana, kuma sun sha soyayya ne na tsawon mako guda kacal.
Aisha ta kasance yarinyar tsohon shugaban karamar hukumar ta Safana a jihar Katsina.
Mai martaba sarikin Daura ya angwance da sabuwar amaryar tasa ne bayan ya auri Aiaha Iro Maikano a watan disemban daya gabata.