Pages

Tuesday 18 October 2016

Rahama Sadau kada ki amsa kiran wani kafiri>> Sako daga malam Aminu Ibrahim Daurawa


Sanannen malamin addini Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa ya aikawa jarumar fim din Hausa da aka kora daga masana'antar fin-finan hausa sannan kuma sanadiyyar korar da aka mata, wani mawakin kasar Amerika me suna Akon ya gayyaceta zuwa can kasar Amurkar dan ta shiga harkar finafinai acan, wannan dai ba kowace face kamar yanda mutane da dama suka sani wato Rahama Sadau.

Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya aike da sakonne ta shafinsa na facebook inda yayi kira a gareta da tayi aure, sannan kada ta amsa gayyatar arne sannan a karshe yayi kira ga mutane dasu isarmata da sakon nashi.

Ga abinda yace a cikin sakon nashi.

"SLM,BUDADDIYAR WASIQA ZUWA GA YAR'WASAN KWAIKWAYON NAN RAHAMA SADAU,
HAKIKA Ki SANI MUSULINCI ADDININE WANDA YA YARDA DA IDAN MUTUM YAYI KUSKURE A KIRASHI A GAYA MASA GASKIYA A TUNATAR DasHI AYOYIN ALLAH, KO YA GYARA, KISANI ALLAH YAYI NUFIN YA JARRABEKI YA GWADA IMANINKI SHI YASA YAN UWANKI MASU HARKA FILM SU KA GUJEKI SAI KUMA GA WASU SUNA NEMANKI, IDAN AL-AMARIN YA INGANTA, TO MU SHAWARAR MU ANAN KARKI AMSA KIRAN WANI KAFIRI DOMIN KE DAI MUSULMACE KUMA MU MUSULINCINKI SHE NE ABIN DUBAWA A GAREMU, DA ZAKIYI AURE MA SHI NE ABINDA YA DACE DAKE. WANNAN HAKKI Ne A KAMMU MU SANAR DA KE ABIN DA ALLAH YA FADA DOMIN AURE SHI NE YA DACE DA YA MACE A KO YAR WAYE A MUSULINCI. WANNAN SAKO NE JAMA'A A ISAR ZUWA GARETA"

Shin Rahama Sadau zatayi amfani da wannan kira da Malam Aminu Ibrahim Daurawa yayimata?

No comments:

Post a Comment