Pages

Saturday 23 December 2017

"Ni ba budurwa bace fil a leda: Na rasa budurcina">>Rahama Sadau

A wata dama data baiwa masoyanta na suyi mata duk tambayar da suke so zata basu amsa, Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci Rahama Sadau ta amsa tambayoyi da yawa, daya daga cikinsu ita wadda wata ta tambayeta, shin ke cikakkaiyar budurwace, ko kuwa kin rasa budurcinki?.



Rahama Sadau ta amsa da cewa, ta rasa budurcinta.

Wasu karin tambayoyin da akawa Rahamar sune:

Wa ya koyamata rawa, ta amsa cewa Ali Nuhu.

Me tafi tsoro a Duniya, tace Mutuwa.

Yaushe zatayi aure, tace kwanannan, amma bata bayyana ko wanene saurayin nataba.

Shin zata iya daina fim?, tace a a.

Dan wasan da yafi birgeta a masana'antar fina-finan Hausa, tace Sadiq Sani Sadiq.

Fim din da tayi wanda tafi so, yafi birgeta, shine fim din turanci na son of the Caliphate.

An tambayeta shekarunta nawa tace, 24.

An tambayeta wane dan wasa take so a masana'antar fina-finan Hausa(Bamu san so na soyayya ta saurayi da budurwaba kokuwa so na son mutum kawai)  tace mawaki kuma sabon jarumi, Umar M. Sharif, dama ta taba fadin wannan a kwanakin baya.

An kuma tambayi Rahama me tafiso a rayuwarta, tace, Mahaifiyarta.

An kuma sake tambayarta, tsakanin mahaifiyarta da mahaifinta wa tafi so, tace mahaifiyarta.

An kuma tambayi Rahama meyasa take son fitowa a fina-finan da bana Hausaba, irin na kasar Indiya dana kudancin kasarnan, wanda hakan ya sabawa addini da al'adar mutanen Arewa, kuma wai anga tallar sabon fim dinta "Dan Iya", Haka  na nufin an dage korar da akayi mata daga masana'antar fina-finan Hausa?

Rahamar ta bayar da amsa ga tambayar sama da cewa itafa 'yar wasan fina-finaice da zata iya yin wasa a ko'ina, bawai masana'anta daya ba kawai, saboda haka tana iya fitowa a cikin fim din kowace masana'anta kuma maganar addini, babu ruwan addini da harkar nishadi, idan kuma mutum yace akwai, to shima duk wace mace da yake da dangantaka da ita kada ya barta tayi kowane irin aiki, domin shima ya sabawa addini, maganar korarl daga masana'antar finafinan Hausa kuwa dama ni ba inda naje.


An kuma tambayeta wai sun sake yin waka tare da mawakinnan da sanadin yin waka dashi aka sallameta daga masana'antar fina-finan Hausa watau Classiq, sai Rahamar tace Eh!.

An kuma tambayi Rahama cewa, wai a lokacin da kuke shirin fim shin sha'awarki tana motsawa, sai tace, Sha'awa kuma? Ko kadan.

An kuma tambayeta mene babban burinta na Duniya, sai ta bayar da cewa, ta zama uwa, watau ta haihu.

An kuma tambayeta ya takeyi da zage-zagen mutane da suke mata a dandalinta na sada zumunta dama zahiri, sai tace kawar dakai kawai take, tayi kamar batajiba.

An tambayeta kin taba yin tunanin canja addini, sai tace, A'A.

An kuma tambayeta shin kina son Annabi(S.A.W)? Sai tace, Eh da dukkan zuciyarta.



No comments:

Post a Comment