Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul Aziz Yari a karshen wannan makon ya yi rijista a matsayin sahihin dan jam’iyyar APC a mazabarsa, garin Talata-Mafara sakamakon ci gaba da rijistar da kuma sake ragin da jam’iyyar APC ke yi.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan rajistarsa tsohon gwamnan wanda shi ne mutum na farko da aka yi wa rajista a jihar ya ce yana da matukar fatan cewa APC za ta samu nasara a jihar a 2023.
Yace; Babu shakka za mu sake kwato ikonmu da aka sata daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar saboda Zamfara ta kasance jihar APC tun daga 1999 cewa Najeriya ta kwato dimokiradiyya daga hannun sojoji”.
Ya kuma bayyana cewa tun daga 1999 har zuwa yau, ba a taba samun nasarar Zamfara a hannun PDP ba, yana mai takaicin cewa abin da ya faru a 2019 sakamakon rashin fahimtar siyasa ne tsakanin mambobin APC wanda aka warware.
Ya kara da cewa, PDP ta kafa gwamnati ta farko a jihar tun daga 1999 tare da taimakon Kotun Koli don samun ikon mallakar jihar baki daya kuma ina tabbatar muku da cewa za mu sake kwato jihar a zabe mai zuwa in Allah Ya yarda”