fbpx
Saturday, May 28
Shadow

2023: Babu zaben fidda gwani bayan 3 ga watan Yuni – INEC ta gargadi APC, PDP, da sauransu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasa cewa ranar Juma’a 3 ga watan Yuni 2022 shi ne wa’adin karshe na gudanar da zabukan fidda gwani na zaben 2023.

Hukumar zaben kasar ta fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis ta hannun shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye.

A cewar Festus Okoye, dukkanin jam’iyyun siyasa na da wata guda daga yau su kammala zabukan fidda gwani.

Ya jaddada cewa ya kamata a gabatar da sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya tsakanin ranakun 10 zuwa 17 ga watan Yuni yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi ya kasance tsakanin 1 zuwa 15 ga watan Yuli.

Leave a Reply

Your email address will not be published.