fbpx
Monday, June 27
Shadow

2023: Duk Sanatocin Bauchi Masu Ci Sun Sha Kaye A Zabukan Fidda Gwani A Mazabunsu

Daga Khalid Idris Doya

Sanatoci guda uku dukkaninsu ‘ya’yan Jam’iuyar APC ne masu ci a halin yanzu daga jihar Bauchi kuma dukkaninsu babu wanda zai sake komawa Majalisar Dattawa ta kasa daga bayan zaben 2023 domin kuwa sun sha kaye a zaben fitar da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar na Bauchi.

Bayanan da wakilinmu ya tattaro daga jihar ta Bauchi ya nuna cewa Sanatoci guda biyu Lawan Yahaya Gumau (Sanatan Bauchi ta Kudu) da Sanata Adamu Bulkachuwa (Sanatan Bauchi ta Arewa) sun fito neman a sake zabensu a wannan kujerun nasu, inda daliget suka yi waje da su ta hanyar kin zabarsu. Yayin da kuma Sanata Halluru Dauda Jika (Sanatan Bauchi ta tsakiya) ya fito neman tikitin gwamna a jam’iyyar APC wanda kuma ya sha kaye.

A zaben da aka gudanar na neman tikitin kujerar Sanata a karkashin jam’iyyar APC, wakilinmu ya labarto mana cewa Hon. Sirajo Ibrahim Tanko ne ya samu gagarumar nasarar lashe zaben tikitin Sanatan Bauchi ta Arewa inda ya kada Sanatan da ke ci a halin yanzu Sanata Adamu Bulkachuwa da mummunan rinjaye saboda daliget sunma ki jefa masa kuri’a gaba daya.

Karanta wannan  "Dalilin dayasa muka cire sunan Ahmad Lawal, Godwill Akpabio da gwamna Umahi a jadawalinmu">>INEC

Sannan a zaben kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu, Hon. Shehu Buba shi ne ya kada Sanatan mai ci, Lawan Yahaya Gumau da kuri’u kalilan.

Sai kuma tikitin Sanatan Bauchi ta tsakiya wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmad Nana, ya samu nasarar kada abokan takararsa da suka hada da Sanata Isa Hamma Misau da Hon. Abubakar Shehu.

Kazalika, Sanatan da ke ci a wannan kujerar ta Bauchi ta tsakiya a halin yanzu, Sanata Halliru Dauda Jika, bai fito takarar Sanatan ba domin ya fito an dama da shi ne wajen neman tikitin APC a kujerar gwamnan Jihar Bauchi wanda kuma ya sha kasa a hannun, Air Marshal Sadiq Baba Abubakar.

Tunin Jam’iyyu suka ja daga na neman nasara a kujerun Sanatan musamman jam’iyyar APC da PDP domin dukkaninsu sun yi zaben cikin gida na sanatoci da za su rike musu tuta a zaben 2023.

Da wannan matakin al’umar jihar Bauchi ke sa ran yin sabbin sanatoci daga Jam’iyyun da za su samu nasara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.