fbpx
Sunday, May 22
Shadow

2023: Hakan ba zai taba faruwa ba – Shugaban INEC ya karyata jita-jitar aniyar tsayawa takarar shugaban kasa

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Yakubu Mahmood, ya musanta rahotannin da ke cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Shugaban a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 8 ga Mayu, 2022 ta hannun babban sakataren yada labaran sa, Rotimi Yekanmi, ya bayyana cewa ba ya sha’awar shiga takarar shugaban kasa.

Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan Najeriya suka mayar da martani da cewa ba abin mamaki ba ne idan shugaban hukumar zabe ta INEC ta bayyana aniyarsa ta maye gurbin Buhari bayan da aka samu labarin cewa gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: La Liga ta kai karan PSG wurin hukumar wasan kwallon kafa ta UEFA bayan Mbappe ya fasa komawa Madrid

Shugaban hukumar ta INEC da ya ke maida martani kan ikirarin ya ce hakan ba za ta taba faruwa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.