Tsohon hadimin gwamman jihar Kaduna kuma malamin addinin Islama, Sheikh Halliru Maraya ya bayyana cewa, masu neman a tsayar da duka ‘yan takarar shugaban kasa Musulmai ko kirista basawa Najariya fatan Alheri.
Ya bayyana hakane a hirarsa da manema labarai.
Yace babu addinin da ya fi wani addini masu kwarewa da ya kamata su yi mulki idandai za’a bi cancantane.
Yace kuma masu neman a yi wannan abu ya kamata su lura da yanda a yanzu kawunan ‘yan Najariya ya rabu sosai wanda hakan zai kara kawo rarrabuwar kawunan ne.