Kungiyar Malaman addinin Kirista reshen Kudu-maso-Kudu ta Najeriya ta jaddada goyon bayan ga tsohon Gwamnan Jihar Legas Mista Bola Tinubu.
Malaman sun bayyana cewa Najeriya na bukatar dan siyasa mai girman kamar Tinubu domin ya zama shugaban kasar.
Malaman sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban kodinetan, Joseph Francis na Delta da mataimakin kodineta, Apostle Chris Ebhodaghe na Edo, suka bayar ga manema labarai a Benin ranar Litinin.
Kungiyar ta bukaci mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da su tabbatar da cewa Tinubu ya samu tikitin jam’iyyar.