fbpx
Sunday, February 28
Shadow

2023: PDP tayi Kira ga Sufeto Janar da aka kama Shugaban Jam’iyyar APC na Kano Kan munanan Kalaman da yayi

Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta rubutawa Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu wasika, ta nemi a kama kuma a gurfanar da shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas a kan munanan kalaman da yayi.

A kwana nan ne, Shugaban APC ta Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya umurci matasan jam’iyyar da cewa a 2023 duk wanda yayi yunkurin yi masu magudin zabe su farmasa kuma babu abunda zai faru.

Da yake maida martani, shugaban jam’iyyar PDP na jihar kano, alhaji shehu wada sagagi, ya ce sun rubuta wasika zuwa ga Sufeto Janar da sauran hukumomin gwamnati da abin ya shafa.

Yace basu yi mamaki ba saboda dabi’ar sa ce ya yi wadannan kalaman masu tunzura matasa.

Ya kuma a wurinsu wannan barazana ce ta banza domin kuwa ba za ta hana mutanen kirki daga jihar Kano zabar mutanen da suke so ba.

Irin wadannan maganganun da ba a kiyaye su suna bukatar a dauki kwararan matakai.

Abbas ya taba yin irin wadannan kalamai ga jam’iyyar mu ta PDP a jihar, wanda hakan yana haddasa rikici a tsakanin matasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *