fbpx
Sunday, June 26
Shadow

2023:”Zamu yiwa yan bindiga aman bamabamai har sai sun gudu”>>Amaechi

Tsohon ministan sufuri, Hon. Rotimi Amaechi ya bayyana cewa zai yiwa ‘yan bindiga aman bamabamai har sai sun gudu idan har aka zabe shi a matsayin shugaban Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a jihar Katsina yayin dayaje ranar litinin domin ganawa da wakilan APC na jihar don su zabe shi a zaben fidda gwani mai zuwa.

Inda yace a lokacin daya zama gwamnan jihar Rivers kashe kashe da garkuwa da mutane yayi yawa sosai a jihar, amma cikin watanni shida ya magance matsalar.

Domin ya hana kanshi bacci kuma ya hana ‘yan ta’addan bacci duk don jama’ar jihar Rivers suyi bacci, kuma bai fara yin bacci ba har sai da yaga ya shawo kan matsalar bakidaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.