fbpx
Saturday, August 20
Shadow

3 da ga cikin Kwankwasiyya Scholars sun shiga jerin masana kimiyya da a ka fi kafa hujja da su a duniya

Uku da ga cikin Kwankwasiyya Scholars sun shiga jerin masana kimiyya guda 20 da a ka fi kafa hujja da sakamakon binciken su a faɗin duniya.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Kwankwasiyya Scholars, wasu ɗalibai ne ƴan asalin Kano da gwamnatin tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ta ɗauki nauyin karatun su a ƙasashen waje, inda su ka yi karatun digiri na biyu, inda su ka kafa kungiya mai suna Kwankwasiyya Scholars.

Har bayan gwamnan ya sauka da ga mulki, sai ɗariƙar sa ta siyasa, wato Kwankwasiyya ta ci gaba da ɗaukar nauyin dalibai karatu a ƙasashen waje.

Da ga cikin su waɗannan ƴan Kwankwasiyya Scholars ukun da a ka fi kafa hujja da su a kwai Dakta Aliyu Isa Aliyu, Dakta Tukur Abdulkadir Sulaiman da Dakta Abdullahi Yusuf.

Jerin sunayen, wanda a ka wallafa shi a watan Agustan 2021, wasu gungun masu bincike ne, ƙarƙashin jagorancin Farfesa John Loannidis a Jami’ar Stanford da ke California a Amurka.

Loannidis da mataimakan sa sun yi amfani ne da wasu manhajoji, in da su ka bi diddigi su ka auna yawan kafa hujja ta ƙashin kai, haɗakar wallafa, wallafar farko, da kuma wata hikima ta bincika masana da abokan bincikensu su ka fi kafa hujja da sakamakon binciken su.

Jerin sunayen ya ƙunshi masu bincike sama da dubu 100 da a ka zaƙulo su daga masana kimiyya sama da miliyan 8 a ɓangarorin kimiyya 22 da sashi-sashi 176 a faɗin duniya.

Karanta wannan  Labari me dadi: An kwato buhunan takin zamani da 'yan ta'adda suka siya dan hada bamabamai

An haifi Dakta Abdullahi Yusuf a Ƙaramar Hukumar Dala a Jihar Kano. Ya kammala digirin sa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil a shekarar 2010. Ya kuma kammala digirin sa na uku, wato PhD a ɓangaren lissafi na musamman a Jami’ar Firat, Elazig, a Turkiyya a shekarar 2019.

Shi kuma Dakta Tukur Abdulkadir Sulaiman, an haife shi ne a Ƙaramar Hukumar Ƙiru a Jihar Kano. Ya kammala digirin sa na farko a Jami’ar Bayero Kano a 2009. Shi ma ya kammala digirin sa na uku, wato PhD a ɓangaren lissafi na musamman a Jami’ar Firat, Elazig, a Turkiyya a shekarar 2019.

An haifi Dakta Aliyu Isa Aliyu a Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano Ya kammala digirin sa na farko a Jami’ar Bayero Kano a 2009. Shi ma ya kammala digirin sa na uku, wato PhD a ɓangaren lissafi na musamman a Jami’ar Firat, Elazig, a Turkiyya a shekarar 2018.

A shekarar 2012 ne dai gwamnatin Kwankwaso ta ɗauki nauyin karatun su na digiri na biyu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke garin Irbid.

Yanzu haka, dukkan Daktocin uku na aiki a Sashin Ilimin Lissafi na Jami’ar Taraiya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.