fbpx
Friday, July 1
Shadow

Dan wasan tsakiya na Barcelona Rakitic ya gayawa kungiyar tashi cewa kar su mayar da shi kamar buhun dankali

Dan wasan tsakiya na Barcelona Rakitic ya kalubalanci kungiyar shi saboda rashin adalcin da suke nuna mai kuma suka so su tilasta mai barin kungiyar a shekarar data gabata. Dan wasan ya kasance a Barcelona tun shekara ta 2014 kuma ya rasa matsayin shi a kungiyar tun da suke siya dan wasan tsakiya na Dutch Frankie de jong.

 

 

Rakitic ya gayawa manema labarai na Mundo Deprotivo cewa ya fahimci abunda Barcelona suke nufi da shi kuma shi ba buhun dankali bane da zasu juya shi yadda suke so, saboda haka yana so ya koma kungiyar da zasu ringa girmama shi, in koma girmamawar tana Barcelona to zai yi farin ciki, in kuma Bata nan to shine ya kamata ya dauki matakin daya kamata ba wani ba.
A shekarar data gabata Barcelona sunyi kokarin amfani da Rakitic domin su dawo da Neymar amma sai Rakitic yaki amincewa ya koma Paris saint German. Yayin da yake cewa yana matukar bakin cikin abun da faru da shi a wannan kakar wasan saboda ya rasa matsayin shi a kungiyar. Amma yace zai tsaya har izuwa 2021 yayin da kwangilar zata kuma haka yana nufin Barcelona ba zasu karbi komai ba in ya shirya barin kungiyar.
Rakitic yace shekarar data gabata itace wadda yafi so a cikin shekaru 6 da yayi a kungiyar amma yayi bakin cikin abun daya faru da shi kuma ya lamarin ya matukar bashi mamaki. Babban abun da yake bashi haushi shine bai yi wasa dayawa a kungiyar.
Barcelona sune a saman teburin gasar la liga kafin a dakatar da wasannin kwallon kafa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Za'a ba wanda ya lashe gasar tseren Marathon dala 80,000 a jihar Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published.