fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Idan kana son ka cigaba da irin wannan rayuwar, to ka bar Najeriya>>Daraktan NCAC, Runsewe ya gaya wa Bobrisky

Darakta-Janar na Hukumar Al’adu Gargajiya ta Kasa (NCAC), Otunba Olusegun Runsewe, ya yi kira ga iyaye da su cusa wa ‘ya’yansu al’adu da dabi’u na Afirka don su girma su zama manya masu da’a.

Runsewe ya fadi haka ne a ranar Lahadi 7 ga watan Fabrairu yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya gargadi iyaye da su kasance suna ba da jagoranci ga ya’yanasu a koda yaushe don tabbatar da cewa ba za suyi ba su yi watsi da al’adun Afirka da ɗabi’un su ta hanyar auratayya, haihuwa, tarbiyantarwa, ɗabi’u da girmama dattawa.

Runsewe, wanda ya ba da misali da salon Okuneye Idris Olarenwaju, wanda aka fi sani da Bobrisky, dan asalin jihar Legas, ya ce Bobrisky ya haifar da matsala ga dabi’un Najeriya da na Afirka yayin da yake yaudarar wasu matasa, saboda da gurbatattun ɗabi’u.

A cewar Runsewe, Bobrisky mai shekaru 29 da haihuwa, abubuwan da yake yi a shafukan sada zumunta abun kyama ne kuma cin mutunci be ga Nageriya da kuma yan Nageriya.

Ya kara da cewa; Harka yan luwadi ko yan daudu ba dabi’ar mu bace, idan har yana son ya cigaba da irin wannan rayuwar to ya bar Nageriya, domin Hukumar NCAC da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya za su hada kai domin yakar wannan musiba.

Runsewe ya yi kira ga iyaye da kada su bar ya’yanasu su koyi munanan dabi’u irin na Bobrisky.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *