fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Kotu ta daure ma’aikacin KNUPDA da ya damfari gwamnatin Kano sama da 500,000

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Mohammed Ibrahim Hassan, ma’aikacin Hukumar Kula da Birane da Bunkasa Jihar Kano (KNUPDA) hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari saboda damfarar Gwamnatin Jihar N513, 445.

 

Hukumar ta ICPC ce ta gurfanar da Hassan a gabanta kan tuhume-tuhume 4 na zarge-zargen yin jabun asusun Gwamnatin Jihar Kano, da nufin tallafawa tare da ikirarin mayar da kudin ga Gwamnatin Jihar.

 

Mai gabatar da karar ya fadawa kotu cewa laifin ya sabawa sashi na 25 (1) (a) na dokokin aikata rashawa da sauran laifuka masu alaka da hakan, 2000, hukuncinsu a karkashin sashi na 25 (1) (b) na wannan dokar, da kuma sashi na 363 na da Penal Code, Cap 105 Laws na Jihar Kano, wanda yake da hukunci a sashe na 364 na wannan dokar.

 

An bayyana cewa Hassan ya aikata laifin ne tsakanin Yunin 2017 zuwa Maris, 2018, lokacin da ya yi rashin gaskiya ya yi rarar baitulmalin Gwamnatin Jihar Kano don tallafa wa da’awar da ya yi na dawo da N299, 509 da N213, 935 a wasu bangarori daban, ga Gwamnatin Jihar.

 

Ya musanta aikata laifin a lokacin da aka karanta masa tuhumar, amma daga baya ya karbi laifinsa ya kuma nemi sassaucin hukunci.

 

Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai shari’a Lawal Wada ya yankewa wanda ake kara hukuncin daurin shekara biyar ko kuma tarar N100, 000.

 

Ya kuma yanke hukuncin tare da umurtar mai laifin ya mayarwa da Gwamnatin Jihar Kano Kudi N513, 445.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *