fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

Korar Fulani Makiyaya: Yan dattawa sun ce takura musu na iya janyo tarwatsewar Najeriya

Wasu sanatoci a majalisar dattawan Najeriya sun buƙaci gwamnati ta gaggauta lalubo bakin zaren warware matsalar uzzurawa Fulani Makiyaya da ake yi a wasu jihohin kudancin ƙasar.

Sanatocin yawancinsu da suka fito daga shiyyar arewacin Najeriya sun yi wannan kira ne a yayin zaman majalisar dattawa a ranar Laraba.

Sun ce akwai barazanar cewa matsin da makiyaya ke fuskanta sakamakon korarsu da gwamnonin wasu jihohi suka yi, da kuma fara kai musu hare-hare na iya janyo babbar barazana ga ci gaba da kasancewar Najeriya a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliya.

Daya daga cikinsu Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nassarawa, ya shaidawa BBC cewa akwai takaici, yadda har aka samu wani gwamna ya fito ƙarara yana kama sunan Fulani yana bayyana su a matsayin ƴan ‘adda.

”Har ta kai yanzu an fara kaiwa Fulani hari ana ƙona muhallansu, amma ba bu wanda ya cewa wannan gwamna ya fito ya nemi afuwa a kan kalaman daya yi, amma mu in muce za mu yi magana sai a riƙa kwaɓarmu, ga wasu suna aikata abin da ya yi dai-dai da ta’addanci ana kallonsuan ƙi a tanka musu” inji shi.

Ya ƙara da cewa dole ne mahukunta su tashi tsaye wajen neman hanyar kawo ƙarshen wannan al’amari tun kafin lokaci ya ƙure.

Shi ma Sanata Ahmed Lawan ɗan majalisar dattawa daga jihar Borno na cikin masu irin wannan kira, kuma ya shaida wa BBC cewa babbar matsalar ita ce ƴan yankin arewacin Najeriya na kallon irin cin kashin da yi wa mutanensu, don haka hakan na iya janyo ramuwar gayya.

Wani abu da ƴan majalisar suka mayar da hankali a kai kuma shi ne yin kiran da a kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke ci gaba da ƙamari a kusan yawancin jihohin Najeriyarya da suka haɗar satar mutane da fashi da makami.

A cewarsu, matsalolin sai ƙara muni ke yi, kasanacewar aƙalla jihohi kimanin tara na fama da hare-haren ƴan bindiga da matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa.

A baya dai ana ganin matsalar ta tsaya ne a jihohin arewa, saɓanin yanzu da ta fantsama har zuwa jihohin kudu.

Bazuwar irin wannan lamari shi ya sa `yan majalisar suka ce ya zama wajibi ga gwamnatin tarayya da ta yi wa tubkar hanci, domin ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka ido.

BBChausa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *