fbpx
Thursday, February 25
Shadow

An gurfanar da mahaifida ya kashe diyarsa da duka

An gurfanar da wani mai gadi mai shekaru 35, Patrick Akpan a gaban kotun majistare da ke Yaba a Legas bisa zargin dukan ’yarsa‘ yar shekara uku har lahira a ranar 27 ga Disamba. 2020.

‘Yan sanda sun gurfanar da Akpan a gaban kotu saboda kisan kai.

Lauya mai shigar da kara, ASP Thomas Nurudeen, ya fadawa kotu cewa Akpan ya aikata laifin ne a Jakande Estate, Lekki phase 1, Lagos, yaa ce Akpan ya lakada wa ‘yarsa duka da bel don ta lalata gidansa.

Yan sanda sun ce yarinyar ta mutu a hannun mahaifiyarta yayin da aka kai ta asibiti.

Ya ce laifin ya sabawa sashi na 224 kuma yana da hukunci a karkashin sashi na 229 na dokokin manyan laifuka na jihar Legas ta shekarar 2015.

Babban alkalin kotun P.E. Nwaka bai yanke wa Akpan hukunci ba, ya kuma tura fayil din karar ga Daraktan Lauyoyin Masu Gabatar da Kara na Legas (DPP) don neman shawara a kan shari’ar.

An daga karar har zuwa ranar 23 ga Fabrairu don neman shawarar DPP

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *