fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Yanzu haka: Makiyaya 4000 ne suka dawo a Jihar Kaduna daga kudu

Kimanin makiyaya 4,000 ne suka yi kaura zuwa jihar Kaduna daga kudu sakamakon umarnin da wasu Gwamnonin jihohin suka bayar ga makiyaya masu aikata laifuka da su bar gandun dazukan jihohin.

An fadawa manema labarai cewa wani mashahuran makiyaya a jihar, wadanda ke yankin Labduga a karamar Hukumar Kachia, ta fara ganin kwararar wadannan makiyaya da shanunsu, tun makon da ya gabata.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) ta tabbatar da faruwar, jami’inta, Hussaini Abdullahi ya ce ya zuwa yanzu sun tabbatar da kimanin 4,000, duk da cewa har yanzu akwai wasu da ke kan hanyar zuwa Kaduna.

Karanta wannan  Kotun daukaka kara ta saka ranar da zata saurari karan mawakin da aka yankewa hukuncin rataya saboda zagin Annabi Muhammadu a jihar Kano

Abdullahi ya kara da cewa, akasarin makiyayan da suka yi kaura sun rasa abin da za su ci don haka suna bukatar abinci da da agajin gaggawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.