Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su hukunta duk wani dan jam’iyyar adawa da aka kama magudin zabe a 2023.
Abbas ya ce ya kamata a afka wa mambobin adawa da aka kama suna magudin kowane zabe ba abin da zai faru.
Shugaban APC din ya yi wannan kiran ne yayin bikin rantsar da sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomin 44 da ke jihar a jiya a Kano.