fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yan Sanda Sun Gano Wani Abun Fashewa Mai Kama da Bam a Jihar Kano

An samu fargaba a ranar Juma’a a garin Jogana, wani yanki da ke tazarar kilomita kaɗan daga birnin Kano, biyo bayan gano wani abun fashewa a Aujirawa Alkali, wani ƙauye da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar.
Masu motocin da ke bin hanyar Hadejia dole suke yi sauri don neman kariya don kar su afka cikin bala’in idan na’urar ta tashi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da rahoton a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
Ya ce, rundunar ta samu nasarar tarwatsa na’urar ne ta hanyar kungiyar masu binciken fashewar abubuwa (EOD), ya kara da cewa an fara bincike don gano wadanda ke da hannu a lamarin.
Ya ce wani mazaunin yankin ne ya gano na’urar a lokacin da ya je daji don sauƙaƙa kansa da misalin ƙarfe 5 na safiyar Juma’a.
Kiyawa ya ce, da ganin na’urar, sai mutumin ya tayar da kara kuma nan take aka sanar da ‘yan sanda lamarin suka tattara suka kewaye yankin.
Ya ce: “Bayan samun wannan bayanin, kwamishinan‘ yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shuaibu Dikko, ya tashi tare da umartar wata tawaga da ke kwance bama-bamai, karkashin jagorancin CSP Haruna Ismail, da su kaura zuwa wurin.
“Nan take tawagar ta shiga aiki bayan da suka kewaye yankin, an gano wata na’urar da ba ta dace ba.
“An kwance abin fashewar cikin nasara tare da amfani da kayan fasaha.
“An fara bincike,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan bindiga sunyi garkuwa da sojan ruwa bayan sun ji masa ciwo da adduna

Leave a Reply

Your email address will not be published.