fbpx
Sunday, May 22
Shadow

A 2050 idan ba a yi taka-tsan-tsan ba, Najeriya za ta zama kasa mafi yawan jama’a a duniya – Hukumar Kidaya ta Kasa

Hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta yi gargadin cewa nan da shekarar 2050 Najeriya za ta iya zama kasa mafi yawan al’umma a duniya.

A cewar Dr Mohammed Abdulmalik Durunguwa, kwamishinan NPC, yawan jama’a a Nageriya abu ne kamar bam ne mai lokaci wanda kuma zai iya tashi a shekarar 2050.

Dokta Durunguwa ya lura cewa ba za a iya kwatanta yawan al’ummar ƙasar da ƴan albarkatun da suke amfani da su ba don haka zai yi wahala a iya ciyar da al’umma gaba ɗaya.

Da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar NUJ, Kaduna a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu, ya ce matasan da ke aikata miyagun laifuka duk wani abu ne na yawan jama’a da ba a kula da su yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.