fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

A America ma ana samun matsalar tsaro amma basu ce shugabansu yayi murabus ba>>Shugaba Buhari

Me magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya caccaki kungiyar dattawan Arewa kan cewar da ta yi shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi murabus saboda matsalar tsaro.

 

Yace kungiyar tana cike ne da ‘yan Bakin ciki da kuma wanda suka nemi mukami a mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari basu samu ba.

 

Yace kungiyar bata da wasu mabiya dake mata biyayya, kamar ace janar din soja ne a fagen yaki da bashi da sojoji.

 

Yace a shekarar 2019 kungiyar ta fito karara ta nuna cewa tana tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

 

Yace da burinta bai cika ba shine ta koma sukar gwamnatin shugaban kasa.

Karanta wannan  Dandazon Mata Sun Yi Bikin Kona Tsintsiyar Jam'iyyar APC A Kaduna

 

Yace matsalar tsaro ba’a Najeriya kadai take faruwa ba, matsala ce data mamaye Duniya, inda a kasar Amurka ma an samu yanda aka rika kashe mutane da yawa amma babu wanda ya fito yace shugaban kasar yayi murabus.

 

Yace masu cewa shugaba Buharin ya sauka kawai suna yi ne dan tunzura ‘yan Najeriya akanshi amma ba zasu yi nasara ba dan ‘yan Najeriyar na da hankali.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.