Monday, March 30
Shadow

A BI DOKA KUMA A TAUSAYAWA TALAKA>>SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

Bayan Kira da muke yi ga al’umma da subi dukkan matakai da jami’an kiwon lafiya suke bayarwa domin kare kai daga yaduwar annoba, da Kuma tuba da yadda da kaddara da addua da istigfari,
A wannan halin firgici na Coronavirus da ake ciki, kamata yayi Shugaban Qasa, Gwamnoni, Y’an Majalisun Tarayya da na Jiha, Sanatoci da sauran manyan muqarrabai na gwamnati su ce a rage musu albashi da allowances ya dawo rabi.

 

Su d’au rabi; rabi kuma a taimakawa talakawan da suke mulka don rage musu rad’ad’in da suke ji. Hakan zai nuna sun damu da su kuma suna tausayinsu . kuma za suji dadin zaman gida.

 

Allah ya yaye mana dukkan balai da musiba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *