Mahaifin matar nan mai juna biyu Harira Jubril da ‘yan bindiga suka kashe tare da ‘ya’yanta hudu a jihar Anambra da ke Najeriya ya nemi hukumomi su biya shi diyya.
Mallam Musa Wakili ya ce tun da lamarin ya faru bai sake yin bacci ba kuma ya nemi gwamnatoci su dauki mataki domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
A jiya laraba ne dai aka yi jana’izar marigayiya Harira da kuma ‘ya’yanta hudu a Awka da ke Jihar Anambra.
Mijin matar kuma mahaifin ƴaƴan dukkanin mata da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa ne da ƴaƴansa a lokacin da suke kan hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai, tare da ƴaƴanta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.
Ya ce ya ji kamar ya haukace saboda tashin hankalin da ya shiga.
Abokin aikinmu Salihu Adamu Usman ya tattauna da mahaifin nata wanda ya fara bayani kan halin da ya shiga tunda lamarin ya faru.