Thursday, July 18
Shadow

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

Gwammatin tarayya a karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen da shugaban kasar ke amfani dasu a cikin watanni 11 da suka gabata.

Hakan na zuwane a yayin da majalisar tarayya ta amince a sayowa shugaban kasar sabbin jirage 2.

Kudin da za’a kashe wajan siyo sabbin jiragen sun kai Naira Biliyan 918.7 ko kuma dala Miliyan 623.4, kamar yanda kwamitin majalisar ya bayyana.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, jiragen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima ke amfani dasu sun tsufa sosai suna bukatar a canjasu.

Karanta Wannan  Hoto:Kasar Ingila ta Haramtawa babban malamin kasar Kuwai, Sheikh Othman al-Khamees shiga kasarta saboda yace Luwadi Haramunne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *