Ranar Talata shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tafi kasar Sifaniya dan ziyarar aiki.
Ana tsammanin shugaban kasar zai dawo Najeriya ranar Juma’a kamin fara zaben fidda gwani na ‘yan takarar shugaban kasar jam’iyyarsa ta APC.
Cikin watanni 5 da suka gabata, shugaban kasar ya je kasashe 8 kenan.
Shugaba Buhari yaje kasar UAE gaisuwar shugaban kasar da ya rasu, hakanan ya je masar Equatorial Guinea inda ya halarci taron AU, hakanan ya je kasar Ivory coast inda ya halarci taron majalisar dinkin Duniya.
Shugana Buhari ya kuma je birnin Brussels na kasar Belgium, a watan Fabrairu, hakanan a watan Maris, shugaba Buhari ya je kasar Kenya.
Hakanan shugaba Buhari ya kuma je kasar Ethiopia, sai kuma birnin Landan na kasar Ingila da yaje can ma aka duba lafiyarsa.