fbpx
Thursday, August 18
Shadow

A dai ci gaba da hakuri da Juriya>>Shugaba Buhari ya gayawa ‘yan Najeriya

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari a sakon taya barka da Sallah ga ‘yan Najeriya ya bukaci su ci gaba da hakuri da juriya da dokokin hana yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19 da aka saka.

 

Shugaban yace dokokin sun hana mutane taruwa kamar yanda aka saba a baya, musamman a guraren Ibada wanda yace amma suna da fa’ida.

Shugaban yace koda ba dan kawunan mu ba ya kamata mu bi dokokin dan na kusa da mu da kuma masoyanmu. Shugaban ya bukaci musulmai da ma sauran mabiya addinai su ci gaba da hakuri gwamnati.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya roki sabon shugaban kirista da sauran malamai su yiwa Najeriya addu'a

 

Ya kuma bukaci musulmai da su yi ko yi da halayen fiyayyen halitta, Manzon Tsira Annabi Muhammad (SAW) a lokacin shagulgulan Sallah.  Yace kuma musulmai su bi dokokin addini yace ya kamata komi mutum zai yi ya zamana yana saka tsohron Allah a ciki.

 

Shugaban ya kuma jawo hankalin ‘yan Najeriya da cewa su lura cutar Coronavirus/COVID-19 ba a Najeriya kadai take ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.