Farfesa Wole Soyinka ya karyata rade-radin da ake cewa wai ya ce a zabi shugaban kasa, Muhammadu Buhari a shekarar 2015.
Farfesa Soyinka yace a wancan karin, cewa yayi kada a zabi Goodluck Jonathan, amma bai ce a zabi shugaba Buhari ba.
Yace yana da ‘yancin da zai zabi wanda yakeso a Najeriya.
Wasu dai musamman ‘yan kudu sun rika caccakarsa kan cewa ya zugasu suka zabi shugaban kasa, Muhammadu Buhari.