Gwamnatin tarayya ta mayarwa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar martani kan caccakar da yawa gwamnatin shugaba Buhari.
A wata ganawa da aka yi da Atiku a kafar talabijin ta Arise TV, Atikun ya bayyana cewa, Gwamnatin Buharin ba ta yiwa kasa aikin da ya kamata ba.
Saidai a martanin ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad, ya fadi cewa Atiku mazaunin Dubai ne dan haka ba lallai yasan abinda ke faruwa a kasarnan ba.
Ya kuma bayyana cewa, Atikun na daya daga cikin ‘yan siyasar dake neman kujerar shugabancin Najariya ido rufe, shiyasa yake irin wannan maganar.